Kamfanin tace mai na Dangote ya sanar da karin sabon farashi ga man fetur, inda ya danganta matakin da hauhawar tashin hankalin siyasa a duniya.
A cikin wata sanarwa da aka aikawa ‘yan kasuwa a daren Juma’a, matatar ta bayyana cewa farashin da take sayarwa daga matata ya tashi daga Naira 1,175 kan kowace lita zuwa Naira 1,245 kan kowace lita, yayin da farashin da ake jigila ta teku shi ma ya karu.
Sanarwar ta nuna cewa karin farashin ya kai Naira 70 kan kowace lita a bangaren matata, yayin da farashin jigilar teku ya karu daga Naira 1,512,648 kan kowace ton zuwa Naira 1,606,518 kan kowace ton.
Matatar ta bayyana cewa sabon tsarin farashin zai fara aiki daga tsakar dare na ranar 21 ga watan Maris, 2026, kuma zai shafi duk kayayyakin da ba a kammala lodinsu ba a matata da kuma wadanda ke kan hanya ta teku.
Haka kuma kamfanin ya bayyana cewa ‘yan kasuwar da suke da yarjejeniyar saye da aka tabbatar da ita ta hanyar banki za su ci gaba da karɓar kayayyaki bisa tsohon tsari, amma dole ne su biya bambancin farashin da aka samu sakamakon wannan karin.
Kamfanin ya kara da cewa za a cire kudin bambancin farashin daga asusun kasuwancin ‘yan kasuwar, tare da bukatar su gabatar da shaidar biyan wannan bambanci kafin ranar Litinin 23 ga watan Maris, 2026.
Ana sa ran wannan karin farashi zai haifar da karin kudin man fetur a gidajen mai a fadin kasa, yayin da ‘yan kasuwa za su dora karin kudin ga masu amfani, abin da ke nuna yadda kasuwar man fetur a Najeriya ke ci gaba da fuskantar tasirin canjin farashin danyen mai a duniya da kuma matsalolin samarwa duk da fara aiki da matatar Dangote.













































