Masu daukar nauyin ayyukan Boko Haram an san su – Buratai

Tukur Buratai 750x430

Tsohon babban hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya, ya bayyana cewa bai kamata a dora masa alhakin rashin fitar da sunayen mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci a kasar ba.

Ya kuma ce ana san masu daukar nauyin, kuma suna cikin al’umma, amma akwai dalilan da suka sa ba a bayyana sunayensu ba.

Yayin wata hira a wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Buratai ya bayyana cewa hukumomin da suka dace sun san wadanda ke bayan daukar nauyin, amma suna da nasu dalilai na kin bayyana su ga jama’a.

Ya kara da cewa daukar mataki shi ne mafi muhimmanci, domin wadannan mutane har yanzu suna cikin al’umma kuma an san su, amma ba shi da alhakin bayyana sunayensu, sai dai abubuwan da suka shafi rundunar sojin kasa kawai.

Buratai ya kuma fayyace cewa shirin gyara halayen ‘yan Boko Haram da suka tuba ba na sojoji ba ne, gwamnati ce ta dauki wannan mataki, inda aka ba su wa’adi a shekarar 2016 su mika wuya, sannan aka mika su ga hukumomin da suka dace domin gyara su.

Ya nuna damuwa kan matsalolin tsaro a kasar, inda ya bukaci a kara karfafa tattara bayanan sirri domin yakar ta’addanci da sauran barazanar tsaro.

Ya kuma bukaci gwamnati ta dauki karin jami’an tsaro domin inganta tsaro a fadin kasar baki daya.

An dade ana kira da a bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci, musamman bayan alkawarin da gwamnatın tarayya ta yi na fallasa tare da hukunta wadanda ke bayan ayyukan ta’addanci.

A shekarar 2021, gwamnatın tarayya ta sanar da cewa ta gano wasu mutane da kungiyoyi da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci, lamarin da ya sa jama’a suka sa ran za a bayyana sunayensu.

Sai dai duk da wannan bayani, har yanzu ba a fito da sunayen wadannan mutane ba, abin da ke jawo suka daga kungiyoyin farar hula da masana tsaro da ke ganin cewa bayyana gaskiya na da muhimmanci wajen kawo karshen rashin hukunta masu laifi.

Najeriya ta shafe sama da shekaru goma tana fama da rikicin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, inda kungiyar Boko Haram da bangarorinta suka haddasa mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa da dama barin muhallansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here