Gwamnatin Tarayya ta umurci Shagunan sayar da magunguna sama da 1,300 da aka rufe a Kano domin su koma Dangwauro

NAFDAC Kano 720x430

Gwamnatin tarayya ta umurci masu shagunan sayar da magunguna 1,321 da aka rufe a Kano, da su koma dangwauro, domin tabbatar da sa ido da kuma kare kasar nan.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) tare da hadin gwiwar hukumar magunguna ta Najeriya (PCN) sun rufe shagunan a ranar 18 ga watan Fabrairu saboda gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba a Kano.

Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali-Pate ne ya bayar da wannan umarni a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya ziyarci cibiyar CWC a ranar Juma’a a Kano.

A cewarsa, tsarin rarraba magunguna wani muhimmin al’amari ne na inganta tsaro da ingancin magungunan da al’ummarmu ke amfani da su.

Ya yi kira ga dillalan magunguna da su bi ka’idoji da kuma bin dokokin da aka tsara.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran, ya ce jihar za ta taimaka wa kananan dillalan magunguna domin samun shaguna a CWC.

” Samun shago a CWC yana daya daga cikin damuwar dillalan magunguna da suka taso yayin ganawarmu da su. Za mu tabbatar mun kubutar da kasuwar mu daga miyagun kwayoyi.”

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here