Uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari, ta yi kira ga Musulmi da su yi amfani da lokacin Azumin watan Ramadana wajen ƙarfafa addu’o’in samun zaman lafiya da tsaro a Najeriya.
Mai ɗakin Buharin ta yi kiran ne a daren Talatar makon nan lokacin da ta karɓi baƙuncin matan hafsoshin tsaro da sauran manyan jami’an gwamnati yayin taron shan ruwa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ta ce, Allah maɗaukakin sarki ya sake bai wa ƴan Najeriya damar sake ganin zagayowar Azumi wanda kuma dama ce ta yin addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Uwargidan shugaban ƙasan ta kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da nuna kyawawan dabi’u soyayya, goyon baya, yafiya da sadaukarwa domin ci gaban ƴan ƙasa da ma Nijeriya baki ɗaya.
Ka zalika da take nuna godiyarta ga Allah madaukakin Sarki da ya ba ta damar ganin zagayowar watan Ramadana na bana, ta bayyana fatan ganin wannan lokacin zai samar wa Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa Azumin watan Ramadana guda ne daga cikin rukunnin addinin musulunci guda biyar da ke bayar da dama ga al’ummar musulmi wajen tsai da sallah cikin kankan da kai da tsoron Allah.
Haka nan kuma lokacin azumi shi ne shimfiɗa kyawawan halaye na rabo, gafara, soyayya, zaman lafiya da sadaukarwa domin ci gaban al’umma.
Manyan baƙi da suka halarci taron sun hada da matan ministoci da sauran matan wasu cikin jiga-jigai a Najeriya waɗanda baki ɗaya suka nuna jin daɗinsu ga uwargidan shugaban kasar bisa jajircewarta na ganin an samu zaman lafiya a Najeriya.













































