Ƴan bindiga sun harbe wani sabon zaɓaɓɓen kansila a jihar Katsina a lokacin da suka kai farmaki daga yammacin Talata zuwa safiyar yau Laraba.
Rahotonni sun bayyana cewa, an kashe kansilan Alhaji Nasiru Magaji, wanda aka fi sani da Nasiru B.S a garin Gozaki da ke karamar hukumar Ƙafur.
Marigayin kansilan, wanda aka harbe shi a gidansa an garzaya da shi asibiti a Malumfashi inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarsa.
Wani mazaunin garin Gozaki mai suna Abdullahi Gozaki ya shaida wa Daily Trust cewa ƴan bindigar da yawansu ya kai goma sun kuma yi awon gaba da matan kansilan, amma daga baya suka sake su.
“Sun kai hari a daren wayewar Laraba da misalin ƙarfe 12:30 inda suka kashe kansila tare da sace matansa biyu amma daga baya suka mayar da su gida,” inji shi.
Ba wannan ne karon farko da za a kai hari garin Gozaki ba, A shekarar da ta gabata dai an yi garkuwa da mutane da dama a yankin ciki har da na sabuwar amaryar wani jami’in shige da fice ta ƙasa.
Ƴan bindigar sun kuma mamaye garin Funtuwa inda shaidu suka ce wasu ƴan bindiga da aka ce kusan 100 ne suka kai farmaki Dutsen Reme da Kauyi da misalin ƙarfe 11:00 na dare, inda suka harbe wani mutum Buhari Amadu wanda aka fi sani da Buhari Michael, ma’aikacin karamar hukumar Bakori, wanda kuma ke yin aikin banga.
Ɓata garin sun kuma kashe wani yaro mai shekaru 10 zuwa 12 mai suna Usman a lokacin harin.
Sun kuma kai hari a unguwar Ɗan Rimi da ke Malumfashi, shalkwatar ƙaramar hukumar Malumfashi, inda shaidun gani da ido suka ce an sace matan wani manajan gidan mai su biyu.













































