Masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, za su biya naira miliyan ɗari domin mallakar fom kafin su shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a watan Mayu.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta APC na ƙasa Felix Morka, ne ya sanar da hakan jim kaɗan bayan kammala taron jam’iyyar na ƙasa karo na 11 a Abuja yau Laraba.
Ya ce an ƙayyade kuɗin fom ɗin na gani ina so na takarar shugaban ƙasa a kan naira miliyan 30 yayin da fom ɗin takarar kuma yake a matsayin naira miliyan 70, wanda jimlar kuɗin suka kama naira miliyan ɗari.
Sakataren yaɗa labaran ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta fara sayar da fom ne a ranar 22 ga wannan wata na Afrilu da muke.










































