Ƴan majalisar tarayya na son a yi bincike kan dala biliyan 25 ta gyaran matatun mai

503cd394 80b1 423c 9c38 1dd292a740b6
503cd394 80b1 423c 9c38 1dd292a740b6

Majalisar dokokin Najeriya ta nemi da a gudanar da bincike na ƙwaƙƙwaf bayan da wani rahotonta ya gano cewa an kashe sama da dala biliyan 25 a cikin shekara goma da ta gabata wajen gyaran matutun man.

Rahoton ya gano cewa duk da wannan ɗimbin kuɗi da aka kashe matatun hudu suna aiki neƙasa da kashi 30 cikin dari.

Wannan batun ya taso ne yayin da farashin mai a ƙasar mai arziƙin mai ya ninka sama da biyu bayan da sabon shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin mai, wanda ya ce kasafin kuɗin da ya gada bai tanade shi ba.

Saboda rashin aikin matatun man yadda ya kamata tsawon shekaru Najeriyar wadda ita ce ta fi kowace ƙasa a Afirka arziƙin man tana fitar da ɗanyen man nata ne ta kuma sayo wanda aka tace daga waje.

A wata mai zuwa ne ake sa ran katafariyar matar man da babban attajirin Afirka Aliko Ɗangote, ya gina a Lagos za ta fara aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here