EFCC ta kama mutum 26 da ake zargi da damfara a yanar gizo a Fatakwal

Internet, EFCC, kama, yanar gizo, damfara, Fatakwal
Jami’an rundunar shiyyar Fatakwal na Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati EFCC, sun kama mutum 26 da ake zargi da damfarar yanar gizo a ranar...

Jami’an rundunar shiyyar Fatakwal na Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC, sun kama mutum 26 da ake zargi da damfarar yanar gizo a ranar 6 ga watan Mayu da 9 ga wata na 2024 a gidan talabijin na Najeriya, NTA da gatari Choba na Fatakwal da kuma jihar Ribas.

An kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri kan zargin da ake yi musu na hannu a ayyukan da suka shafi intanet.

Karin labari: ‘Yan Sanda a Kano na binciken mutuwar jami’in kwastam da ake zargin ya kashe kansa

Kayayyakin da aka kwato daga wajensu nau’ikan wayoyi ne daban-daban da kwamfutoci da manyan motoci guda shida

Za’a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here