Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kaddamar da bincike kan lamarin mutuwar jami’in hukumar kwastam.
Hakazalika, rundunar ta ce tana binciken mutuwar wasu matasa biyu a ranar Lahadin da ta gabata yayin fadan daba a unguwar Darmanawa da ke jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin.
Karin labari: Karin Kudin Lantarki: NLC ta rufe ofisoshin NERC
Sanarwar ta ce, “A ranar 06/05/2024 da misalin karfe 12 na dare, an samu rahoton cewa jami’in hukumar kwastam, CSC Abdullahi Abdulwahab Magaji da ke aiki a Abuja, da kuma wani mazaunin Farm Center a Kano ya kashe kansa ta hanyar harbin kansa da bindigar aiki.
SolaceBase ta rawaito cewa bisa bincike an gano cewa wani Muhammad Barde mai shekaru 59 dan yankin Darmanawa ya shirya wani taron Gangi na bikin daurin auren ‘ya’yansa da ke tafe inda ‘yan barandan suka farwa junansu.
Karin labari: Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC sun bayyana zuwa ofishin NERC da DisCos
Wanda ya yi sanadiyar raunata mutane uku tare da lalata wasu motocin da ba su ji ba ba su gani ba.
“Saboda haka, Kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin kama wanda ya shirya, Mohamed Barde, tare da wasu mutane biyu da ake zargin suna hannun ‘yan sanda don gudanar da bincike.
Fadan dai ya yi kamari ne bayan ‘yan sa’o’i wanda ya kai ga baje kolin makamai da ‘yan dabar suka yi da wasu jami’an tsaro da suka mayar da martani domin kwantar da hankula.
Karin labari: “A dakatar da tallafin wutar lantarki” – IMF ta bukaci Gwamnatin Tarayya
Wannan ya kai ga mutuwar wani Sadiq Abdulkadir, mai shekaru 23 dan yankin Darmanawa da Muhammad Sani mai shekaru 22 dan unguwar Sallari a Kano.
‘Yan sanda na ci gaba da gudanar da cikakken bincike a halin yanzu a kan al’amuran biyu wanda za’a bayyana cikakken bayaninsu nan gaba.