![Karin Kudin Lantarki: NLC ta rufe ofisoshin NERC NLC, NERC, rufe, ofisoshi, lantarki](https://solacebasehausa.com/wp-content/uploads/2024/05/NLC-sabo-696x464.webp)
A safiyar ranar Litinin ne shugaban NLC Joe Ajaeron, ya jagoranci jami’ansa inda suka je suka rufe ofishin NERC da ke Abuja.
Kungiyar ƙwadago ta rufe ofisoshin Hukumar Wutar Lantarki (NERC) da na kamfanonin rarraba wutar domin nuna adawa da karin kuɗin da aka yi wa ’yan Najeriya.
A Kaduna kuma NLC ta rufe ofishin kamfannin rarraba wutar lantaki ta Kaduna Electric, a wani bangare na zanga-zangar.
Karin labari: Kungiyar likitocin Najeriya ta nada Bala Audu sabon shugaban kungiya
Haka ma kungiyar ta rufe ofishin NERC Jos, fadar Jihar Filato, inda ta hana ma’aikatan hukumar shiga ofisoshinsu don gudanar da aiki.
Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun isa ofisoshin domin dakile tashin rikici ko karya doka da oda.
Tun a ranar Lahadi kungiyoyin kwadago a Najeriya suka yi barazanar rufe ofisoshin NERC da na kamfanonin rarraba wutar lantarki a fadin Najeriya da nufin ganin an soke karin kudin wuta da aka yi.
Karin labari: Kungiyoyin kwadago a Najeriya NLC da TUC sun bayyana zuwa ofishin NERC da DisCos
Ninka kudin wuta da aka yi a watan Afrilu dai ya sha Allah-wadai daga al’ummar Najeriya, inda daga bisani majalisar dokokin kasar ta ba da umarnin a soke.
NERC ta sanar da rage kudin da Naira 19 ga masu amfani da layin Band A wadanda da farko ta yi wa karin kudin kilowatt daga Naira 67 zuwa Naira 225.
Ragin Naira 19 da NERC ta yi a makon jiya dai bai gamsar da jama’ar kasar ba.
’Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tsadar rayuwa a kasar, wanda ta samo asali daga janye tallafin man fetur kafin daga bisani gwamnatin kasar ta janye tallafi a bangaren wutar lantarki.