Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, ya kammala shirye-shiryen bayar da tallafin karatu ga dalibai 1,000 don yin karatun digiri a fannonin da suka shafi fasahar zamani, ICT, ƙarƙashin Gidauniyar Barau I Jibrin, BIJF.
Wadanda za su ci gajiyar shirin su ne daliban da su ka fara karatu a cibiyoyin karatu guda bakwai a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma da ke Jihar Katsina da za a kafa a mazabar Kano ta tsakiya da ta Kudu daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Mai baiwa mataimakin shugaban majalisar dattijai shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, ya ce Sanata Barau da mahukuntan jami’ar sun kammala shirye-shiryen kafa cibiyoyin karatu a mazabun biyu.