Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wasu maza biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifin kiran wata mata mai suna Dahare Abubakar, mai shekaru 67 mayya tare da daba mata wuka har sai da ta mutu.
Wadanda ake tuhumar sun hada da Da’luta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu, da Ayuba Abdulrahman, kuma kotun ta yanke musu hukuncin laifin kisan kai.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Usman Na’abba ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar da ake yi ba tare da wata shakka ba, sannan an yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wadanda aka kama su biyar da laifin.
“Na yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wadanda ake tuhuma da laifin kisan kai, sannan na wanke Nabi’a Ibrahim, wacce ake kara ta shida, kamar yadda shaidu suka nuna,” in mai Shari’a.
Karin labari: Zargin badaƙala: Kotu ta tsare tsohon shugaban NHIS a gidan gyaran hali na Kuje
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Barista Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2023, a kauyen Dadin Kowa da ke Wudil a Kano.
Ya ce wadanda ake tuhumar sun hada baki ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar bayan sun zargi Dahare Abubakar da cewa mayya ce, inda suka bi ta zuwa gona suka kashe ta da muggan makamai.
Daga nan ne aka garzaya da ita zuwa babban asibitin Wudil dake Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwar ta, sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashe na 221 (a), wanda aka karanta da sashe na 79 na dokokin Penal Code na jihar Kano na shekarar 1991.NAN