Kungiyar kwadago ta ƙasa NLC ta samar da dakatar da yajin aikin da ta kudiri aniyar tafiya, biyo bayan karin kudin kiran waya da na data da gwamnatin tarayya ta yi.
Matakin janye yajin aikin ya biyo bayan wata ganawa da suka yi da wakilan gwamnanti a ofishin sakataren gwamnati a daren Litinin tare da cimma matsaya kafin ganawa ta gaba.
Da yake yiwa yan jarida karin bayan ki shugaban NLC Joe Ajaero, ya ce gwamnati ta amince da kafa wani babban kwamiti da zai nazarci duk wasu ɓangarori na yin karin kudin kiran waya sa na Data.
Majalisar Wakilai ta roƙi NLC ta fasa yajin aiki kan ƙarin kuɗin waya
A cewarsa, kwamitin zai kunshi wakilai biyar daga bangarorin biyu kuma ana sa ran zai mika sakamakon bincikensa cikin makonni biyu.
Ajaero ya bayyana cewa, “Mun jaddada cewa NLC ita ce kungiya mafi girma a Afirka, kuma babu wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki da za a yi ba tare da mu ba”.
“A kan haka, sun amince da kafa wani babban kwamiti don tabbatar da daidaito da kuma yarjejeniya mai zurfi don duba tsarin jadawalin karin kuɗin don fito da wata yarjejeniya mai ma’ana”.
Ya kara da cewa matakan da kungiyar za ta dauka na gaba ya dogara ga rahoton kwamitin, da suka hada da zanga-zanga, kauracewa zuwa aiki.