
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da mutum 104 da ake zargi ƴan daba ne a gaban wasu kotuna da ke Nomandsland.
An kama mutanen a wuraren hawan sallah da masarautun Kano ke yi duk shekara a bukukuwan sallah.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Fesbuk inda ya ce ana zargin mutanen da laifukan daba da riƙe makamai da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Karin labari: Gwamnan Kano ya nada sabbin kwamishinoni 4 ciki har da Mustapha Kwankwaso
Kiyawa ya ce an samu kama mutanen ne bayan binciken da aka yi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar kamar yadda kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ya umarta.
A baya-bayan nan ma rundunar ƴan sandan ta Kano ta kama wasu da ta ce ƴan daba ne waɗanda kuma suke addabar unguwar Ɗorayi.