Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Alhamis ya rantsar da sabbin kwamishinoni hudu da majalisar dokokin jihar ta wanke kwanan nan.
SolaceBase ta rawaito cewa sabbin kwamishinonin guda hudu sun hada da Mustapha Rabiu Kwankwaso, guda daga cikin da ga dan takarar shugaban kasa na NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sauran sun hada da Abduljabbar Garko da Shehu Aliyu Yarmedi da kuma Adamu Aliyu Kibiya.
Karin labari: AGF ta nemi tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello da ya mika kansa ga EFCC
Bayan rantsar da su, Gwamna Yusuf ya baiwa sabbin mambobin majalisar zartarwa na jihar mukamai kamar haka:
1- Mustapha Rabiu Kwankwaso – Matasa Da Wasanni
2- Abduljabbar Garko – Kasa da Safiyo
3- Shehu Aliyu Yarmedi – Ayyuka na Musamman
4- Adamu Aliyu Kibiya – Kasuwanci da Masana’antu