Mai Shari’a James Omotosho ya bayar da umarni ga jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS su fitar da Nnamdi Kanu daga harabar kotu saboda rashin biyayya da ya nuna a zaman ranar Alhamis.
Alkalin ya bayar da wannan umarni ne bayan da Kanu ya dage cewa ba za a ci gaba da hukuncin da aka shirya za a karanta a gaban kotun ba a wannan rana.
Shugaban Haramtacciyar ƙungiyar IPOB ya tsaya a matsayinsa tare da kin barin kotu duk da roƙon da jami’an tsaro suka yi masa domin ya saurari umarnin kotu.
Alkalin ya dakatar da zaman bayan ganin yadda Kanu ya ƙi bin tsarin da kotu ta gindaya.
Daga nan sai ya umurci jami’an tsaro su fitar da Kanu daga cikin kotu domin ci gaba da gudanar da sauran lamurra cikin tsari.
A cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, alkalin ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da cewa zaman kotu ya gudana ba tare da tsaiko ba.













































