Babbar Kotun Tarayya ta tabbatar da laifin ta’addanci ga Nnamdi Kanu

nnamdi kanu sad 2

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƴantacciyar Biafra Nnamdi Kanu ya aikata laifi a ƙarƙashin sakin layi na ɗaya na tuhumar ta’addanci da gwamnatin tarayya ta gabatar a kansa.

Kotun ta bayyana cewa ta gamsu cewa Kanu ya yi jerin magana a gidajen yaɗa labarai domin tayar da tarzoma da hallaka mutane yayin fafutukar ballewar Biafra.

Alkalin da ke sauraron shari’ar James Omotosho ya danganta hukuncin nasa ga hujjojin da ɓangaren ƙara ya gabatar wa kotu waɗanda ba a karya su da wata shaida ta daban ba.

Alkalin ya yi watsi da hujjar Kanu cewa ba za a iya ci gaba da shari’ar ba saboda an gina tuhumar ne bisa doka ta hana ta’addanci ta shekarar 2013 da aka soke daga baya.

Kotun ta ci gaba da gudanar da shari’ar bisa ga hujjojin da aka gabatar da kuma tabbatar da cewa akwai gamsuwa a kan tuhumar da ake masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here