Hisbah ta kama wadanda ba sa yin azumi a jihar Kano

hisbah, kama, kano, azumi, ramadan
Hukumar Hisbah ta kama mutane 11 a ranar Talata waɗanda aka ga suna cin abinci a lokacin azumin watan Ramadan a jihar Kano. Kano guda ce daga cikin mafi...

Hukumar Hisbah ta kama mutane 11 a ranar Talata waɗanda aka ga suna cin abinci a lokacin azumin watan Ramadan a jihar Kano.

Kano guda ce daga cikin mafi rinjayen musulmi kuma ta kasance mai aiki da dokokin shari’a da tsarin addinin musulunci.

Hukumar ta hisbah kan gudanar da bincike a wuraren cin abinci da kasuwanni duk shekara a cikin watan Ramadan.

Karin labari: Hukumomin Tigray na ƙasar Habasha sun ce an kori tsoffin ‘yan tawaye 100,000

Kakakin hukumar, Lawal Fagge ya shaidawa manema labarai cewa an kama mutum 11, maza 10 da mace ɗaya da ba sa yin azumi.

“Mun kama mutane 11 a ranar Talata ciki har da wata mata da ke sayar da gyaɗa da aka ga tana cin kayanta inda wasu kuma suka sanar da mu.

“Mutum 10 duk maza ne 1 ce mace a cikin su, kuma an kama su a fadin birnin musamman kusa da kasuwannin da ake tafka ta’asa” in ji shi.

Karin labari: ‘Ƴan sanda sun kama jami’in da ya harbi wani mutum a kasuwar Wuse

Amma ya ce daga bisani an saki waɗanda aka kama bayan sun yi rantsuwar cewa ba za su sake shan azumi da gangan ba.

Ya kara da cewa za’a ci gaba da gudanar da bincike amma ya ce an keɓe waɗanda ba musulmai ba.

“Ba mu kama waɗanda ba musulmai ba saboda wannan bai shafe su ba kuma kawai lokacin da za su iya yin laifi shi ne idan muka gano suna dafa abinci don sayarwa musulmi da ya kamata yana azumi.”

Karin labari: “Yadda na sulale daga hannun ‘ƴan fashin daji” – Ɗalibi

Kimanin shekaru 20 da suka gabata ne aka ɓullo da shari’ar Musulunci domin ta dace da dokokin da ba ruwansu da addini a jihohi 12 na arewacin Najeriya, waɗanda galibinsu Musulmi ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here