Babbar shari’ar miyagun kwayoyi da ake yi wa Abba Kyari na ci gaba da gudana – NDLEA

Abba Kyari sabo

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa babbar shari’ar da take yi wa dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari kan zargin fataucin miyagun kwayoyi na ci gaba da tafiya, kuma za a ci gaba da sauraron ta a kotu ranar 16 ga Maris.

Hukumar ta ce za a ci gaba da shari’ar a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ta jaddada cewa wannan shari’a ta bambanta da wata daban wadda aka sallami Kyari a cikinta kwanan nan.

NDLEA ta yi wannan karin bayani ne bayan hukuncin da mai shari’a James Omotosho ya yanke, inda ya sallami Kyari daga tuhume-tuhume guda 23 da suka shafi zargin wankiyar kudade da kuma rashin bayyana kadarori da hukumar ta shigar a kansa.

Darakta mai kula da kafafen yada labarai da wayar da kai na NDLEA Femi Babafemi ya bayyana cewa hukuncin da mai shari’a Omotosho ya yanke bai kamata a rikita shi da babbar shari’ar miyagun kwayoyi da ake yi wa dakataccen jami’in ‘yan sandan ba.

Labari mai alaƙa: Kotu ta yi watsi da shari’ar Abba Kyari da ‘yan uwansa kan rashin bayyana kadarori

Ya kuma jaddada cewa shari’ar fataucin miyagun kwayoyi na ci gaba da gudana kuma za a ci gaba da sauraron ta kamar yadda aka tsara a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Babafemi ya kara da cewa tawagar lauyoyin da ke gabatar da kara za su nazarci cikakken hukuncin kafin su yanke shawarar ko za su kalubalanci hukuncin da ya sallami Kyari ko a’a.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa Kyari, tsohon shugaban sashen binciken leken asiri na rundunar ‘yan sandan Najeriya, na fuskantar shari’a daga NDLEA kan zargin hannu a laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here