An yi kiki – kaka a zaman kotun yau, wanda Diyar Gwamnan kano Hajia Balaraba Ganduje da akafi sani da Asiya ta shigar tana neman kotu da ta tsinke alakar auren su da mijinta.
Alkalin kotun shari’ar Musulunci dake nan Kano, Khadi Abdullahi Halliru yayin zaman ya umarci ‘yan jarida da su fice daga zauren na sa domin sauraron karar da Asiya-Balaraba Ganduje diyar gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ta shigar.
Jaridar solacebase ta rawaito Alkalin nacewa “wannan shari’a ce ta musamman da ba za a kai rahoto ba” saboda mutanen da abin ya shafa.
Don haka ya zabi sauraron wannan kara a asirce a zaurensa.
Rahotanni sun ce ‘yar gwamnan ta roki kotu da ta yi amfani da tsarin addinin musulunci na khul’i don raba auren shekaru 16 da mijinta, Inuwa Uba, saboda ta “gaji da auren”
Sai dai agefe guda mijin mai suna Uba ya dage cewa har yanzu yana son matarsa kuma ya nemi kotu ta ba shi lokaci don bincika hanyoyin shawo kan matarsa ta soke hukuncin da ta yanke.
Da yake yanke hukunci kan karar, alkalin kotun ya baiwa mijin tsawon makonni biyu ya nemo hanyoyin sasantawa da matarsa, sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Janairu domin yanke hukunci.
Wata majiya mai tushe ta shaidawa wannan jarida cewa, a lokacin da ‘yar gwamnan ta yanke kaunar raba auren da mijin na ta, akayi arba an tura jami’an tsaro dauke da makamai suka kutsa cikin gidan ma’auratan da ke Technical Staff Quarters, tare da kwashe takardun mallaka na kadarorin Mista Uba.
Kaddarorin a cewar majiyoyin sun hada da wani kamfanin sarrafa shinkafa da ke kan titin Kano zuwa Zaria, wurin tarukan biki, takaddun wani gida a Abuja, gidajen mai da dai sauransu.













































