Ƙungiyar malaman jami’oi a Najeriya, ASUU ta yanke shawarar tsawaita yajin aikin da take gudanarwa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa matakin ya zo ne bayan wata zazzafar tattaunawa da aka yi ranar Litinin game da yadda za a cimma matsaya tsakanin ƙungiyar da kuma gwamnati.
An ɗauki matakin ci gaba da yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar ASUU da ke Jami’ar Abuja, babban birnin Najeriya.
Ƙungiyar ASUU dai ta shafe watanni tana gudanar da yajin aikin da ya tilastawa ɗaliban jami’oin gwamnati zama a gida.
ASUU na ganin gudanar da yajin aikin ne hanyar samun mafita ga tarin buƙatun da ta gabatar wa gwamnatin Najeriya ciki har da batun inganta musu albashi.












































