Yadda Karatun Dubban Daliban Firamare a Jihar Kano Ya Tsaya Cak, Sun Gaza Samun Damar Shiga Sakandare

kano schools
kano schools

Dubban daliban da suka kammala karatun firamare a Kano ne suka gaza samun damar shiga makarantar sakandare ba tare da wani laifi na su.

Karatun daliban, wadanda sa’anninsu dake makarantu masu zaman kansu suka riga suka fara sabon zangon karatu, ya tsaya ne cak, saboda gazawar gwamnati na gudanar da jarabawar kammala makarantar firamare ta Common Entrance.

Solacebase ta bada rahoton cewa, kamata ya yi a ce daliban sun rubuta jarabawar da hukumar kula da ilimi ta Kano (KERD) ke shiryawa, tare da jarabawar Gwamnatin Tarayya ta shiga makarantun Unity, tsakanin watan Yuni da Yulin bana.

Sai dai, makonni biyu bayan komawa makaranta a zangon karatu na farko, har yanzu daliban sun gaza ganin cikar burinsu na kasancewa a ajin sakandare.

Lamarin na da rikitarwa, idan aka yi la’akari da umarnin da gwamnati ta bayar cewa, daliban sun koma ajinsu na karshe wato aji 6 na firamare, har zuwa lokacin da za ta gudanar da jarabawar.

Wani malami a daya daga makarantun gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce “an mayar da daliban aji na 7, inda suke zuwa su yi zamansu da abokansu suna hira da wasa”
Ya ce haka aka yi a zangon karatu na baya, inda aka samu jinkirin shigar yaran da suka kammala firamare, ajin sakandare.

Malam Lawan, wanda mahaifi ne ga daya daga cikin daliban da batun ya shafa, ya ce ya dakatar da dansa daga zuwa makaranta, domin rage kashe kudi.

“muna jiran gwamnati ta sanya ranar jarabawa, a sannan ne kadai zai koma makaranta. Ba zan iya ci gaba da biyan kudin mota yana zuwa wasa da hira ba. Sun ki su gudanar da jarabawar shiga sabon aji”

Ko da Solacebase ta tuntubi ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta wayar tarho, game da rashin gudanar da jarabawar, kakakin ma’aikatar Aliyu Yusuf, ya bayar da amsa ta sakon kar ta kwana.

Aliyu Yusuf, wanda bai bayar da wani dalili na jinkirin ba, ko kuma lokacin gudanar da jarabawar, ya ce “bangaren da lamarin ya shafa na shirye-shiryen sanya ranar gudanar da jarabawar”.

Galibin mutane sun yi ammana cewa, wannan wata koma baya ce ga harkar ilimi a yankin, wanda dama ke fama da kalubalen tsaro kamar na satar mutane dake kai wa ga rufe galibin makarantun dake wajen manyan birane.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here