Gwamnatin Sudan Ta Bankado Wani Yunkurin Juyin Mulki

AP 21039667920500
AP 21039667920500

Hukumomi a kasar Sudan, sun bankado wani yunkurin juyin mulki, inda a yanzu yanayin kasar ke karkashin ikon gwamnatin.

Kakakin gwamnatin kasar, Mohamed Suleiman, ya ce za a fara yi wa wadanda ake zargi da hannu cikin juyin mulki tambayoyi, inda rundunar soji za ta fitar da sanarwa bada jimawa ba.

Karanta Wannan: Kogi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Guda Tare da Awon gaba da Mutum 2 a Mujami’a

Wata majiya daga gwamnatin da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce daga cikin yunkurin juyin mulki, har da kokarin kwace iko da gidan rediyon kasar dake Omdurman.

A cewar majiyar, an dauki matakan kame ‘yan tsirarun mutanen dake da hannu cikin lamarin.

Wani ganau a Sudan din ya shaida cewa, da safiyar yau Talata, sojoji sun yi amfani da tankoki wajen toshe gadar da ta hada biranen Omdurman da Khartoum.

Sudan ta kasance karkashen yarjejeniya mara kwari ta raba iko tsakanin sojoji da fararen hula, bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a watan Afrilun 2019.

Hukumomin rikon kwarya na kasar, sun ce ko a baya, sun gano ko bankado yunkurin juyin mulki daga sojoji magoya bayan Omar al-Bashir.

(Reuters/NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here