Kwamitin Gwamnatin Kano na yaki da shaye-shaye da kwacen Waya ya kama matasa 4 da Adaidaita Sahu 2

Tricycles new

Kwamitin gwamnatin jihar Kano na yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi da kuma kwacen Waya, ya kama wasu mutane hudu da ake zargin masu satar wayoyi ne tare da kwace wasu baburan adaidaita sahu guda biyu.

Daraktan hulda da jama’a da wayar da kan al’umma na ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyuka na musamman Malam Muhammad Dahir Idris, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Talata.

SolaceBase ta ruwaito cewa an kama wadanda ake zargin ne a titin zuwa Hadejia da kuma titin Eastern Bypass da misalin karfe 8:00 na dare yayin wani aiki na hadin gwiwa da kwamitin ya gudanar.

A cewar shugaban kwamitin Janar Gambo Ahmad Mai’adua mai ritaya, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin tsere wa bayan sun kwace waya daga hannun wani mutum da ke wucewa.

Ya kara da cewa an kuma gano wasu baburan Adaidaita Sahu wadanda ake zargin cewa, ana yin amfani da su wajen aikata laifin.

Haka kuma, kwamitin ya kara da cewa, kan titin na zuwa Hadejia, an kama wasu karin mutane biyu da ake zargi da kai hari kan wani jami’in tsaro, wanda a yanzu haka yake samun kulawa likitoci.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da ayyuka na musamman, AVM Ibrahim Umaru mai ritaya, ya yaba da kokarin rundunar tare da jaddada kudirin gwamnati na tallafawa ayyukan tsaro a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here