Wata babbar kotun Majistare da ke Sakkwato ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin daurin shekaru hudu da rabi kowanne saboda yada bidiyon tsiraici.
Kotun ta yankewa Aminu Yahatu-Tafida, Umar Abubakar da Mas’ud Gidado hukunci, dukkansu mazauna Sokoto, bayan ta same su da laifin sayarwa da yada littattafan batsa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa an fara gurfanar da masu laifin ne a ranar 5 ga Oktoba, 2020.
Laifukan sun sabawa Dokar Penal, Dokokin Jihar Sakkwato.
Mai gabatar da kara, ASP Samuel Sule, tun da farko ya shaidawa kotun cewa wani mazaunin garin Bardon Barade, Sokoto ne da aka sakaya sunansa ya kawo karar.
Sule ya ce Hayatu-Tafida wanda aka fi sani a Baffa, a shekarar 2017, ya yaudari wata ‘yar shekaru 16 da haihuwa zuwa Otal din Phoenix Guest Inn, inda ya nadi bidiyon tsiraicinta mai tsawon dakika 18 ba tare da saninta ba.
A cewarsa, Hayatu-Tafida ya hada baki da sauran abokansa wajen yada bidiyon a kafafen sada zumunta.
Ya kara da cewa lamarin ya haifar da dakatar da auren wadda lamarin ya shafa run a watan Oktoba 2020.
Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun Majistare Shu’aibu Ahmad, ya ce ya yi la’akari da bukatar wadanda aka yankewa hukunci na neman sassauci inda suka bayyana cewa wannan ne karon farko da suka taba aikata irin hakan.
Ahmad ya yankewa musu hukuncin daurin shekaru biyu kowannensu saboda aikata alfasha da rashin da’a, tare da zabin biyan tarar Naira Dubu dari biyu (200,000).
Ya kuma yanke musu hukuncin daurin shekaru biyu kowannen saboda siyarwa da yada abubuwan da ba su dace ba, da kuma Karin ɗaurin wata shida kowannensu, tare da zaɓi na biyan tasa ta Dubu Hamsin (N50,000) ga kowane laifin.
Ya yi fatan hukunce -hukuncen za su zama izina ga wasu.
Ahmad ya kuma umarci kowanne daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin ya biya N100,000 ga wanda ya shigar da kara a matsayin diyya.
NAN













































