Gwamnan Edo ya bada umarnin gudanar da bincike kan kashe matafiya yan Arewa

Monday Okpebholo 750x430

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya yi Alla-wadai da kashe wasu matafiya da aka yi a garin Uromi da ke ƙaramar hukumar arewa maso gabashin Esan a ranar Alhamis da ta gabata 27 ga Maris, inda ya bayyana kisan da na dabbanci.

Ana ta dai yaɗa wasu faya-fayan bidiyo, wanda a ciki aka nuna wasu matasa sun zagaye wasu mutane da ake tunanin mafarauta ne ƴan arewa da suka taso daga kudancin ƙasar za su koma gida wataƙila domin bikin sallah.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan jihar, Fred Itua ya fitar, ya ce, “Binciken farko-farko ya nuna cewa matafiya ne da suka taso daga Fatakwal na jihar Rivers suka ratso ta garin, sai ƴan banga suka kama su da tunanin cewa ɓatagri ne.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here