A ranar Juma’a ne wata babbar kotun jihar Kano ta yanke wa wata matar aure Fadila Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin yin garkuwa da wata yarinya ‘yar shekara takwas a cikin rijiya, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.
Wadda ake tuhumar da ke zaune a unguwar Sabuwar Gandu, Kano, an same ta da laifin yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Yusuf Muhammad-Ubale ya ce masu gabatar da kara sun tabbatar da shari’ar ba tare da wata shakka ba, sannan kotu ta yanke wa wadda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya.
“Na yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wadda ake tuhuma da laifin yin garkuwa da ita da kuma jefa wadda aka kashe a rijiya, wanda ya yi sanadin mutuwarta.”
Karin karatu: Da ɗumi-ɗumi: Rundunar ƴan sanda ta dakatar da hawan Sallah a Kano
Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Yulin 2019, a yankin Tudun Wada Quarters, Kano.
Ya ce da misalin karfe 4:45 na yamma wadda ake zargin ta yi garkuwa da karamar yarinya ta kai ta gidanta.
“Wadda ake tuhumar ta shaida wa ‘yar uwarta cewa marigayiyar diyar kawarta ce, wadda mahaifiyarta ta yi tafiya zuwa Ghana, kuma ta bukaci ta rike yarinyar har sai ta dawo.
“A ranar 17 ga Yuli, 2019, da misalin karfe 6:30 na yamma, wacce ake kara ta yi sanadin mutuwar karamar yarinya lokacin da ta jefa ta cikin wata zuzzurfar rijiya da ke yankin Tukuntawa a Kano,” in ji shi.
Abba-Sorondinki ya gabatar da shaidu bakwai da suka hada da bayanan wadanda ake kara da kuma rahoton likitan da ke tabbatar da mutuwar wadda aka kashe, sai dai wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashe na 274(b) da 221(a) na kundin laifuffuka.
Lauyan wadda ake kara, Zulaihat Tata, ta gabatar da shaidu hudu, ciki har da wadda ake kara, don bayar da shaida a kan kare ta.(NAN)