Ku maido da kudaden alhazan da kuka gaza yin jigilar su zuwa aikin hajjin 2022-Kungiyoyi.

NAHCON 1 1
NAHCON 1 1

Masu aiko da rahotannin alhazai masu zaman kansu sun bukaci hukumar alhazai ta Najeriya da ta dena 6ata lokaci ta kuma gaggauta maidawa maniyyatan da ta gaza jigilarsu zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin hajji a shekarar 2022.

Kungiyar farar hulan mai zaman kanta, mai fafutukar tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin al’amuran aikin hajji a Najeriya da kuma kare jin dadin alhazai, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kodinetan ta na kasa Ibrahim Muhammad ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, “Ba lallai ba ne NAHCON ta tura makamancin haka don dawo da maniyyatan kudaden su da aka kasa kaiwa kasar saudiyyan Shekarar 2022 duk da cika dukkan sharrudan da ake bukata. ”

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne kungiyar ta IHR ta fitar da sanarwa ga jama’a inda ta bukaci hukumar jin dadin alhazai ta kasa da ta jiha da su cika alkawarin da suka dauka ta hanyar mayar wa maniyyatan da suka biya kudin aikin hajji Naira miliyan 2 da Dubu 500 amma suka kasa zuwa aikin hajjin sakamakon gazawar hukumar nayin jigilar su zuwa kasa mai tsarki.

Bayan sa’o’i 24, hukumar a cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar a fusace ta ce, “a zahirin gaskiya ta nuna shakku kan cancantar kungiyoyin fararen hula na nuna damuwa a madadin daruruwan mahajjata kan gazawar hukumar ta mayar da kudaden maniyyata 67 kwanaki bayan kammala aikin hajjin 2022 a hukumance.”

“Saboda haka, wannan abin mamaki ne matuka hukumar ta kara kaimi wajen ganin an mayar wa ‘yan Najeriya da suka kasa zuwa aikin hajji nan kamar yadda shugaban NAHCON ya yi alkawari.

“Muna tunasar da Uwargida Usara cewa Shugaban Hukumar Barr Zikirullah Kunle Hasan ne ya yi alkawarin fara aikin dawo da kudaden maniyyatan nan bayan aikin Hajjin 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here