
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta zargin cewa jami’anta sun kashe Dakta Chike Akunyili da wani jami’in tsaro a Anambra a ranar 28 ga watan Satumba.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Dakta Peter Afunanya, ya karyata hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce hakan ya biyo bayan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa jami’an DSS sun kashe kunyili, matar marigayi Dr Dora Akunyili, tsohon Ministan Yada Labarai.
“An jawo hankalin hukumar DSS kan zargin cewa jami’anta sun kashe Dakta Chike Akunyili da jami’in tsaro a Nkpor, Anambra a ranar 28 ga Satumba.
A cewar sanarwar “DSS tana musanta waɗannan zarge -zargen kuma tana bayyana wa duniya cewa ba gaskiya ba ne.
“Babu wata hujja da za ta sa DSS ta kashe mutum ko wani jami’in tsaro,” in ji shi.
A cewar mai magana da yawun, DSS na baiwa rayuwa mahimmanci kuna tana bin dokoki.
Afunanya ya bukaci jama’a da su yi watsi da labaran karya daga wadanda ke son amfani da DSS don rufe munanan ayyukansu.
Mai magana da yawun hukumar ta DSS ya ce kokarin da masu laifin ke yi na karkatar da hankula ko sauya tunanin dan adam don yaudarar jama’a da ba a san su ba ya zama kasuwanci a wajensu.
Ya ce nan ba da jimawa ba za a kamo masu laifin.
Afunanya ya kara da cewa hukumar da takwarorinta na tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bibiyar wadanda ke aikata laifukan bata gari a sassan kasar nan. (NAN)












































