Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bai wa hukumar yaki da rashawa ta ICPC damar shiga tare da yin nazari kan na’urorin lantarki da aka kwato daga gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta bayar da umarnin bayan lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da bukatar a gaban kotun.
Lauyan ya roki kotun ta bai wa hukumar damar shiga cikin na’urorin domin duba su tare da gudanar da binciken kimiyya da kuma fitar da bayanai daga cikinsu domin ci gaba da binciken da ake yi kan tsohon gwamnan.
Rahoton ya nuna cewa jami’an hukumar sun kwato kusan na’urorin lantarki guda 14 a lokacin da suka gudanar da bincike a gidan El-Rufai da ke Abuja.
Na’urorin da aka kwato sun hada da na’urar ajiya ta Sony HD-EGS, na’urar ajiya ta ITB Transcend, na’urar ajiya ta Toshiba, wayar Samsung, wayar Nokia N958GB, wayar Blackberry da kuma wayar Google IDEOS.
Sauran sun hada da na’urar ajiya ta Samsung SPO802N, kwamfutar hannu ta Remarkable, kwamfutar kirar Apple MacBook Pro baki, na’urar Seagate FreeAgent Desk external drive, wayar ZTE, sandunan ajiya guda 10 da kuma katin ƙwaƙwalwar Microcell.
Shari’ar bukatar kotun ta ICPC tana dauke da lamba FHC/ABJ/CS/499/2026 tsakanin Tarayyar Najeriya da Nasir Ahmad El-Rufai.
A halin yanzu kuma El-Rufai yana gaban wannan kotu inda yake kalubalantar binciken da aka yi a gidansa tare da neman a biya shi diyyar naira biliyan 1.
A cikin karar kare hakkinsa ta asali, tsohon gwamnan ya sanya ICPC, babban alkalin kotun majistare ta birnin tarayya Abuja, Babban sufeton ‘yan sanda na kasa da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya a matsayin wadanda ake kara na farko zuwa na hudu.
El-Rufai ya bukaci kotun ta bayyana cewa shiga gidansa da aka yi tare da binciken gidan da ke lamba 12 titin Mambilla, Aso Drive, Abuja a ranar 19 ga Fabrairu da misalin karfe 2 na rana ta hannun ICPC da Babban sufeton ‘yan sanda babban take hakkin sa ne na kundin tsarin mulki.
Ya kuma roki kotun ta bayyana cewa duk wata hujja da aka samo sakamakon wannan sammacin bincike da ya kira mara inganci ba za a iya amfani da ita a kowace irin shari’a a kansa ba.
Ya kuma nemi kotun ta bayar da umarnin hana wadanda ake kara su ci gaba da amfani da duk wata hujja ko kayayyakin da aka kwato daga gidansa a duk wani bincike ko shari’a da ya shafe shi.
Haka kuma ya bukaci a mayar masa da dukkan kayayyakin da aka kwato daga gidansa tare da cikakken jerin su, sannan a ba shi diyyar naira biliyan 1 a matsayin diyya ta gaba daya da kuma ta musamman.
Sai dai a cikin martanin da ta gabatar, ICPC ta bayyana cewa ta samu korafi kan El-Rufai kuma bisa wannan korafi ne ta fara bincike wanda ya kai ga gudanar da binciken a gidansa.
Hukumar ta ce jami’anta sun gudanar da aikin ne bisa sahihin sammacin bincike da kotu ta bayar a ranar 18 ga Fabrairu kuma aka aiwatar da shi a ranar 19 ga Fabrairu tsakanin karfe 1:37 na rana zuwa 3:56 na rana a lamba 12 titin Mambilla, Asokoro, Abuja.
Ta kuma ce jami’an hukumar sun je wurin tare da jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya, kuma matar El-Rufai Hadiza El-Rufai da dansa Mohammed El-Rufai sun halarci lokacin da aka gudanar da binciken.
Rundunar ‘yan sanda ta kuma bayyana a cikin takardar martaninta cewa tana da ikon gano masu laifi, kama su, gudanar da bincike a kansu da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Ta kara da cewa binciken da aka yi a gidan El-Rufai an gudanar da shi ne bisa sahihin sammacin bincike da kotu mai iko ta bayar, tana mai jaddada cewa sammacin na sahihi ne.
A cewar rundunar, jami’anta sun bi dukkan ka’idojin doka da suka dace yayin aiwatar da sammacin binciken.
Rundunar ta kara da cewa mai karar na kokarin amfani da kotu domin kare kansa daga binciken tsaro da kuma gurfanar da shi a gaban kotu.
Don haka ta roki kotun da ta yi watsi da karar baki daya.













































