Gwamnatin jihar Kogi ta haramtawa sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma bayar da wasikun amincewa ga masu hakar ma’adinai a jihar.
Gwamnati ta ba da umarnin cewa daga yanzu duk takardar amincewa dole ta bi ta hanyar da ta dace don yin nazari akan ta.
Karanta wannan: INEC ta dakatar da zabe a wasu wurare a jihar Kogi
Kwamishinan ma’adanai da albarkatun kasa Alhaji Bashir Gegu, ne ya bayyana hakan lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya kan batutuwan da suka shafi bada takardun amincewa da yarjejeniyar ci gaban al’umma a Lokoja.
Kwamishinan ya bayyana cewa: “Wannan matakin da gwamnati ta dauka ya zama wajibi bisa la’akari da yanayin da ake ciki game da bayar da takardun amincewar.” Ya ce irin ta’asar da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ke yi ne ya sanya aka hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar.
Karanta wannan: Mutane 8 sun rasa rayukansu sakamakon hadarin mota a jihar Kwara
Kwamishinan ya shaida wa sarakunan cewa suna nan a sahun gaba na masu ruwa da tsaki a harkar gina tattalin arziki da zaman lafiyar ko wanne yanki.
Ya kuma bada tabbacin gwamnati zata ci gaba da bawa sarakunan goyon baya a kokarin da suke yi na dakile rikice-rikicen kabilanci da ke ci gaba da janyo hasarar rayuka da lalata dukiyoyi.
A cewarsa, yana da matukar muhimmanci su ci gaba da wanzar da zaman lafiya a fadin jihar domin cimma muradun tabbatar da ci gaban al’umma musamman na jihar Kogi da Najeriya baki daya.
Ya ce gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar ma’adanai za ta ci gaba da samar da tsare-tsaren da za su samar da yanayin da fannin hakar ma’adanai zai samar da gagarumin ci gaba a jihar.
Dangane da yarjejeniyar ci gaban al’umma kuwa, Gegu ya ce dokar ta tanadi cewa kafin kowane kamfani ya fara aikin hakar ma’adinai, sai ya gabatar da takardun muhalli da suka wajaba Kafin fara aiki.
Ya koka da yadda akasarin masu zuba jari a fannin hakar ma’adanai ke gaza cika ka’idojin muhalli ta fuskar samar da ruwan sha da samar da wutar lantarki da ayyukan kiwon lafiya da sauransu.
Gegu ya ce gwamnatin jihar ta hannun ma’aikatar za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki da kuma kamfanonin hakar ma’adinai don tabbatar da cikakkiyar yarjejeniyar ci gaban al’umma da za ta yi tasiri ga bangarorin biyu.













































