Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da zabukan da aka gudanar a unguwanni tara na karamar hukumar Ogori/Magongo a jihar Kogi.
Kwamishinan yada labarai na kasa na INEC Mohammed Kudu Haruna ya tabbatar da dakatarwar a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
A cewarsa, an dauki wannan matakin ne saboda rahotannin da aka bayar na “na tabka kura-kurai a zaben, musamman lamarin da ya faru na takardar sakamakon da aka kammala kafin kada kuri’a”.