An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo

jihar ogun, oluomo, tsine, kakakin
Daga Jihar Ogun Mambobin majalisar 18 daga cikin 26 ne suka tsige Oluomo a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Mrs Bolanle Ajayi (APC-Yewa ta Kudu)...

Daga Jihar Ogun Mambobin majalisar 18 daga cikin 26 ne suka tsige Oluomo a yayin zaman da mataimakin kakakin majalisar, Mrs Bolanle Ajayi (APC-Yewa ta Kudu) ta jagoranta.

Sakamakon haka ‘yan majalisar sun zabi Mista Oludaisi Elemide (APC-Odeda) a matsayin sabon shugaban majalisar.

Wani dan majalisa, Mista Adegoke Adeyanju (APC-Yewa North 1) ne ya gabatar da kudirin a tsige Oluomo, yayin da Mista Ademola Adeniran (APC-Sagamu II) ya goyi bayansa.

Karanta wannan: Gwamnatin Taraba ta haramta hawa babura a birnin Jalingo

NAN ta ruwaito cewa Adeyanju ya shiga zauren majalisar ne da katsalandan, tare da wasu ‘yan majalisar.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaben sa a matsayin sabon shugaban majalisar, Elemide ya ce ya kamata al’ummar jihar su yi masa fatan alheri.

“Mu ‘yan majalisa ne masu bin doka da oda. Muna son duniya ta sani cewa yanzu an samu sauyi a shugabancin majalisar,” inji shi.

Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Filato Mutfwang ya ayyana dokar hana fita ta sa’o’i 24

Elemide, wanda ya ce ‘yan majalisa 18 ne suka goyi bayan fitowar sa a matsayin shugaban majalisar, ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankalinsu.

“Muna hannun dukkan hukumomin gidan. Muna ba da tabbacin cewa sabon shugaban zai goyi bayan gwamnan mu, Prince Dapo Abiodun.

“Ina tabbatar muku cewa gwamnan bai san komai ba game da wannan tsigewar,” in ji shi.

Shi ma da yake magana, Mista Damilola Soneye (APC-Obafemi Owode) ya lura cewa ya kamata kakakin majalisar ya zama na farko a cikin masu daidaitawa.

Karanta wannan: AA Rano ya kaddamar da sabon dakin karbar magani a AKTH wanda Sanata Ibrahim Shekarau ya gida

“An tsige shugaban majalisar ne saboda rashin da’a da kwantar da kai da rashin mayar da hankali da gaskiya tare da nuna isa da kuma rashin salon shugabanci, har ma da almubazzaranci da kudi da kuma tunzura ‘yan uwa a kan juna,” in ji Soneye.

Haka kuma shugaban majalisar da aka tsige, Oluomo bai halarci zaman majalisar ba, yayin da duk kokarin jin ta bakinsa kan lamarin ya ci tura, saboda kiraye-kirayen da aka yi a wayarsa da dama ba su gudana ba.

A karshe magatakarda da mataimakin magatakardar majalisar, Mista Deji Adeyemo da Misis Funmilayo Adeyemi bi da bi sun kasance a zauren taron, yayin da aka lura da jami’an tsaro da yawa a harabar majalisar kamar yadda NAN, ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here