Majalisar dokokin Zamfara ta tsige jagoran marasa rinjaye, Aliyu Ango-Kagara

Zamfara Assembly

 

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta bayyana kujerar jagoran marasa rinjaye, Aliyu Ango-Kagara, a matsayin wacce ta zama babu kowa a kanta saboda yawan kin halartar zama.

A zaman da aka yi a Gusau ranar Talata, majalisar ta ce Ango-Kagara (APC-Talata-Marafa South) bai halarci zaman majalisar na tsawon kwanaki 159 ba.

Jagoran masu rinjaye, Bello Mazawaje, ya gabatar da bukatar a ayyana kujerarsa a matsayin babu kowa a kanta, yana mai cewa dan majalisar ya halarci zaman majalisa 21 kacal daga cikin 180 tun bayan rantsar da su.

Duk da cewa wasu ‘yan majalisar kamar Halliru Kuturu sun bukaci a dauki matakin ladabtarwa maimakon tsige shi, amma Kakakin Majalisar, Alh.

Bilyaminu Moriki, ya bayyana cewa dole ne su aiwatar da tanadin kundin tsarin mulki, kuma ya ayyana kujerar Ango-Kagara a matsayin babu kowa a kanta.

A martaninsa, Ango-Kagara ya ce matakin da aka dauka ba bisa doka ba ne, yana zargin cewa an yanke masa hukunci saboda goyon bayansa ga ‘yan majalisar da aka dakatar bisa batun tsaro a yankunansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here