Shekara 61 da samun ƴanci: Murtala Garo ya buƙaci a haɗea kai wajen ƙara gina Najeriya

E671E099 F7F9 4B14 B8AC 99985BCF5ED9 cx0 cy6 cw0 w408 r1 s
E671E099 F7F9 4B14 B8AC 99985BCF5ED9 cx0 cy6 cw0 w408 r1 s

Kwamishinan Kananan hukumomi da al’amuran masarautu na jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo, ya yaba wa ƴan Najeriya bisa jajircewa da gudunmawar da suka bayar wajen ci gabanta tun bayan samun ƴancin kai.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne ta cikin saƙon taya murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ƴancin kai, Alhaji Murtala Sule Garo ya nanata buƙatar zaman lafiya da lumana, domin kuwa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba matuƙar tana cikin yanayi maras daɗi.

Garo ya ce duk da cewa Najeriya ba ta cimma wasu burin ci gaban ta ba tun bayan samun ‘yancin kai, amma dai ta yi wasu manyan abubuwan da ba za a manta da su ba.

Haka kuma, ya buƙaci ƴan Najeriya da su cigaba da yin addu’a ga Najeriya don shawo kan ƙalubalen tsaro, tare da jajircewar kowane ɗan kasa da kuma bada goyon baya ga jami’an tsaro ta yadda kasar za ta fita daga cikin wannan matsala.

Kwamishinan ya jinjina wa ci gaba da kuma salon jagorancin gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

A cewarsa, ci gaban da gwamnatin jihar ta samu tare da yaɗuwar ayyuka a cikin ƙananan hukumomi 44 a cikin shekaru 6 na gwamnatin abin a yaba ne.

“Kasancewar gwamna Ganduje a matsayin jagoran zazzaga ayyukan zamani a Kano, ayyukansa na raya kasa ba su mai da hankali a cikin birni ba, don haka, ba a bar kowacce ƙaramar hukuma ta jihar da wani shiri ko wani ba,” in ji Murtala Sule Garo.

Haka kuma ya yi kira ga mutane da su ci gaba da tallafa wa gwamnatin domin yin tarin ayyuka da kuma kammala ayyukan da ke yankunan su tare da sanya ido akan ayyukan domin daƙile maɓarnata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here