Tinubu ya taya Flamingos murnar lashe kofin kofin duniya

Flamingos

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya taya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Flamingos, murnar zama ƙungiyar Afirka ta farko da ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata ta ‘yan ƙasa da shekara 17.

Flamingos ta doke Japan da ci 2-1 a wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya ta matan ta shekarar 2026, wanda aka buga a ranar Asabar a birnin Rabat na ƙasar Morocco, inda ta lashe kofin gasar a karon farko a tarihin ƙasar.

Shugaban ƙasar, wanda ya samu labarin nasarar bayan dawowarsa daga yaƙin nrman zaɓe a jihohin Akwa Ibom da Rivers, ya bayyana nasarar a matsayin wani abin alfahari ga Najeriya.

Haka kuma, ya bayyana nasarar a matsayin wani gagarumin tarihi ga ƙwallon ƙafar mata a nahiyar Afirka.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Asabar.

“Wannan labari ne mai daɗi da na dawo gida na tarar da shi. ’Yan matanmu sun yi nasara a duniya, sun kuma ba ’yan Najeriya a ko’ina wani sabon dalilin yin bikin ƙasarmu mai girma.

“Ga jaruman Flamingos, ina taya ku murna. Kun nuna jarumta, ladabi, jajircewa da ruhin Najeriya na rashin yanke ƙauna.

“Na bibiyi tafiyarku a duk tsawon wannan gasa, kuma bayan nasarar da kuka samu a wasan kusa da na ƙarshe, kun yi alƙawarin kawo kofin gida.

“Yau kun cika wannan alƙawari. Kun yi imani da kanku, kun yi yaƙi domin juna, sannan kun ɗaga tutar ƙasarmu zuwa kololuwar duniya.

“Nasararku abin koyi ce ga miliyoyin ’yan matan Najeriya da ke da burin cimma manyan nasarori.

“Kun nuna musu cewa da aiki tuƙuru, samun dama da jajircewa, su ma za su iya kaiwa matakin nasara mafi girma.

“Yau Najeriya na alfahari da ku. Kun rubuta sunayenku da zinare, kuma ƙasarku na matuƙar alfahari da ku,” in ji shi.

Tinubu ya yaba musamman ga Awawu Bashiru da Oluebube Umejiaku, waɗanda suka ci ƙwallayen da suka tabbatar da wannan gagarumar nasara, tare da yabawa sauran ’yan wasan bisa kyakkyawar haɗin kan da suka nuna.

Haka kuma, ya taya masu horar da ’yan wasan, Hukumar Kula da Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) da Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC) murnar irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar ƙungiyar.

Shugaban ƙasar ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na haɓaka harkokin wasanni daga tushe, tare da faɗaɗa damar da matasan Najeriya, musamman ’yan mata, za su samu wajen gano basirarsu, haɓaka ta da kuma cimma burinsu.

“na sake taya ku murna, Flamingos. Na gode da sanya Najeriya alfahari.” (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here