Kano: Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa bisa laifin kashe uwa da ’ya’yanta shida

Hanging rope

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa Umar Auwal da Yakubu Dayyabu hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi da ke Kano.

Alkalin kotun mai lamba 11, Mai Shari’a Nasiru Saminu, ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamban 2026, bayan nazarin hujjoji da shaidun da aka gabatar a yayin shari’ar.

Kotun ta samu Auwal, wanda aka fi sani da Breaker, da Dayyabu, wanda aka fi sani da Wawo, da laifin kashe Fatima da ’ya’yanta shida a ranar 17 ga Janairun 2026.

Saboda haka, kotun ta yanke wa kowannensu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Haka kuma, kotun ta yanke musu hukuncin ɗaurin rai da rai bisa laifukan haɗa baki da fashi da makami.

Sai dai Mai Shari’a Saminu ya wanke tare da sallamar mutum na uku da ake tuhuma, Isiyaku Yakubu, daga zargin haɗa baki da kisan kai.

Tawagar lauyoyin gwamnati da suka jagoranci shari’ar ta ƙunshi Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabir Maude, tare da Lauya Salisu Muhammad Tahir.

A cewar Antoni Janar ɗin, hukuncin kotun ya tabbatar da matsayin masu gabatar da ƙara kan rawar da waɗanda aka yanke wa hukuncin suka taka wajen kisan da kuma fashi da makami.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar a shirye take ta bi matakan aiwatar da hukuncin kisa idan waɗanda aka yanke wa hukuncin suka gaza amfani da damar ɗaukaka ƙara cikin wa’adin da doka ta tanada.

Maude ya yabawa rundunar ’yan sanda bisa gudanar da bincike mai zurfi, tare da jinjinawa jami’an Ma’aikatar Shari’a kan gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da hukuncin.

Dangane da wanda aka sallama, Maude ya bayyana cewa duk da kotu ta wanke Isiyaku Abdul’azeez a wannan shari’ar, har yanzu yana fuskantar wasu shari’o’i biyu daban-daban, waɗanda ake sa ran yanke musu hukunci nan gaba.

Lauyoyin da suka kare waɗanda ake tuhuma su ne J. I. Musa da A. I. Baba.

SolaceBase ta tuna cewa an kashe Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a ranar 17 ga Janairun 2026, a gidansu da ke unguwar Dorayi Chiranchi a Kano, lamarin da ya janyo matuƙar damuwa a tsakanin al’umma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here