Hukumar Kula da Shari’a ta Ƙasa (NJC) ta dakatar da wasu jami’an shari’a uku na tsawon shekara guda ba tare da albashi ba, tare da yi wa wasu takwas kashedi kan aikata laifuffuka daban-daban da suka haɗa da tsare waɗanda ake yi wa shari’a ba bisa ƙa’ida ba, amfani da ikon kotu ta hanyar da ba ta dace ba da kuma yin watsi da ƙa’idojin shari’a.
Hukumar, ƙarƙashin jagorancin Alƙalin Alƙalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere Ekun, ta kuma amince da aika wasiƙun gargaɗi ga wasu alƙalai uku bayan gudanar da bincike kan ƙorafe-ƙorafe da suka shafi yadda suka gudanar da shari’o’i.
Read also: Uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu ta isa Kano
An yanke waɗannan hukunci ne a taronta na 112 da aka gudanar a ranar 3 ga Nuwamba, 2026.
Alƙalan da aka dakatar su ne Mai Shari’a Hannatu Mohammed Kabir ta Babbar Kotun Jihar Nasarawa, Babban Kadi Mohammed Sani Salihu na Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Jigawa da Mai Shari’a Sobere Biambo na Babbar Kotun Jihar Rivers.
An dakatar da Mai Shari’a Kabir ne bisa bayar da umarnin kama wani da ake yi wa shari’a da kuma tsare shi na tsawon kwanaki 58 bisa zargin rashin bin umarnin kotu, ba tare da fara sahihin tsarin shari’ar raina kotu ba ko kuma tura masa takardar sanarwar da doka ta tanada, wato Forms 48 da 49.
Hukumar ta kuma hana ta samun damar zaɓen ta zuwa wani matsayi na gaba na tsawon shekaru uku, tana mai cewa matakin nata ya tauye haƙƙin mutumin na samun adalci.
An dakatar da Babban Kadi Salihu ne bisa rawar da ya taka wajen sake buɗe wani hukunci da Kotun Upper Area ta Abuja ta yanke.
Bincike ya gano cewa ya wuce iyakar ikonsa ta hanyar kafa kwamiti domin sake nazarin hukuncin, sannan ya miƙa batun ga wani alƙali daban, wanda ya saurari sabbin shaidu tare da yanke wani sabon hukunci.
Hukumar ta ce wannan tsari ya zama kamar ɗaukaka ƙara a kan sahihin hukuncin wata kotu mai hurumin yin hakan.
Read also: Kano: Hashim ya miƙa ragamar Ma’aikatar Muhalli ga Kachako
Shi kuwa Mai Shari’a Biambo, an hukunta shi ne saboda bayar da umarnin kama waɗanda ake yi wa shari’a da kuma cin tararsu Naira 300,000 kowannensu a wani rikicin shari’ar farar hula, ba tare da bin tsarin shari’ar raina kotu ko yi musu takardun da doka ta tanada ba.
An kuma hana waɗannan alƙalai biyu samun ɗaukaka matsayi na tsawon shekaru uku.
Hukumar ta kuma yi wa Mai Shari’a Kayode Agunloye na Babbar Kotun Abuja kashedi kan yadda ya gudanar da shari’ar neman karɓar kuɗi daga hannun wani banki bayan an riga an yanke hukunci, a wata ƙara da ta shafi First Bank of Nigeria Plc.
An kuma aika wasiƙun gargaɗi ga Mai Shari’a Danjuma Oyigbenu da Mai Shari’a Isa Ebini Kana saboda yanke hukunci a wata ɗaukaka ƙara bayan wa’adin kwanaki 90 da kundin tsarin mulki ya tanada.
Sauran alƙalan da aka yi wa kashedi ko kuma aka sanya cikin jerin sa ido na hukumar sun haɗa da Mai Shari’a Mohammed Zubairu na Babbar Kotun Abuja, saboda bayar da umarni bayan an sanar da shi cewa an shigar da ɗaukaka ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Haka kuma, an yi wa Mai Shari’a C. A. Ogbuagor na Babbar Kotun Jihar Enugu kashedi saboda ci gaba da shari’a duk da cewa akwai ɗaukaka ƙara da buƙatar dakatar da aiwatar da hukunci da ke jiran sauraro.
An kuma yi wa Mai Shari’a Chibuike Azuama na Babbar Kotun Jihar Imo kashedi saboda bayar da umarnin wucin gadi ta hanyar ex parte na dakatar da asusun kamfanin Puma Energy, wanda ba ya cikin waɗanda aka shigar da ƙara a kan batun farko.
NJC ta kuma duba ƙorafe-ƙorafe 35 da kwamitocinta na tantance ƙorafe-ƙorafe suka gabatar, inda ta yi watsi da 24 saboda rashin hujja, ta bayar da shawarar gudanar da ƙarin bincike kan huɗu, sannan ta dakatar da ɗaya saboda yana gaban kotu.
Read also: Kotunan Tafi-da-gidanka ta KAROTA ta kama direbobi 84 da suka karya doka a Danja
NJC ta kuma amince da sanarwar ritayar jami’an shari’a shida, ciki har da alƙalan Kotun Ƙoli biyu, tare da miƙa ta’aziyyarta kan rasuwar jami’an shari’a tara tsakanin watan Mayu da Satumba na shekarar 2026.













































