Hukumar kula da Zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta ce kotunan ta na tafi-da-gidanka sun kama direbobi 84 da suka karya dokokin amfani da Danja a cikin birnin Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Ibrahim, ya bayyana cewa kotunan sun yanke wannan hukunci ne a zaman da suka gudanar na tsawon kwana biyu a wurare daban-daban na cikin birni.
A zaman kotun da aka gudanar a kan titin Filin Jirgin Sama kusa da shatale-talen Baban Gwari ƙarƙashin jagorancin Alkalin Babbar Kotun Majistare Halima Wali, direbobi da masu keke Napep 41 aka samu da laifi.
Karin labari: Hukumar kiyaye haddura ta kasa ta kaddamar da wata manhaja Domin Rage Hadarorin Hanya
Haka kuma, wani zama a kan titin Zoo Road kusa da Gidan Buhari ƙarƙashin jagorancin Alkalin Majistare Hauwa Abba ta kama masu laifi 43.
Daraktan Hukumar KAROTA, Malam Faisal Kabir, ya bayyana cewa kotunan tafi-da-gidanka za su ci gaba da gudanar da zaman a wurare daban-daban domin rage laifukan zirga-zirga.
Ya ce manufar ba don takura masu amfani da hanya ba bace, illa dai domin tsabtace zirga-zirga da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma, bisa manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Ya yi kira ga direbobi da su rika bin dokoki da ƙa’idojin zirga-zirga a koda yaushe.
(NAN)













































