Ƙungiyar ma’aikatan Man Fetur da iskar Gas (NUPENG) ta zargi kamfanin Dangote da karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a hedikwatar hukumar tsaro ta DSS a ranar 9 ga Satumba, 2025.
Ƙungiyar ta gargadi cewa hakan na iya tilastwa ta dawo da yajin aikin da ta dakatar a baya.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Prince Williams Akporeha, tare da sakataren janar, Afolabi Olawale suka sa hannu, NUPENG ta umarci mambobinta a fadin ƙasa su kasance cikin shiri don komawa yajin aiki idan aka tilasta. Sun ce yarjejeniyar da DSS ta jagoranta tare da ministoci uku na tarayya da babban jami’in DSS ta amince wa ma’aikata da ‘yancin kafa ƙungiya.
Sai dai ƙungiyar ta ce a ranar 10 ga Satumba, kamfanin Dangote ya umarci direbobin manyan motoci da dama, waɗanda galibinsu ‘ya’yan NUPENG ne, da su cire tambarin ƙungiyar daga motocinsu.
Washegari kuma aka umarce su da su tilasta shiga harabar kamfanin don ɗaukar kaya, amma aka hana su shiga saboda keta ƙa’idojin lodin kayayyaki.
Karin labari: Babu gudu ba ja da baya kan batun yajin aiki – NUPENG ta nanata
NUPENG ta bayyana hakan a matsayin raini ga hukumomin gwamnati da dokokin ƙasa, tana mai gargadin cewa babu wanda ya kamata a ba dama ya keta yarjejeniyar da gwamnati ta amince da ita. Ta kuma roƙi gwamnatin tarayya da ta hana amfani da jami’an tsaro wajen tauye haƙƙin ma’aikata.
Ƙungiyar ta yi kira ga NLC, TUC, ƙungiyoyin farar hula da ƙungiyoyin kwadago na ƙasa da na duniya da su nuna goyon baya a wannan rikici.
Ta kara da cewa dukiya ba za ta taɓa ɗaga wani sama da doka ba.
A cewar NUPENG, suna da kishin ƙasa kuma za su ci gaba da zama masu alhakin kare martabar Najeriya da walwalar jama’a.
Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, kamfanin Dangote bai bayar da martani ba.











































