Babu gudu ba ja da baya kan batun yajin aiki – NUPENG ta nanata

NUPENG 2

ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ta tabbatar da cewa ba za ta janye daga yajin aikin da ta tsara ba a ranar Litinin, saboda kin amincewar kamfanin mai na dangote da ya bari direbobin motocin cng da aka shigo da su su shiga cikin ƙungiyar.

Ƙungiyar ta ce rassa na direbobin manyan motoci masu ɗaukar mai za su daina aiki da jigilar mai daga ma’ajiyoyin kasa baki ɗaya.

NUPENG ta yi watsi da wata sanarwa da shugabannin wata ƙungiya mai suna direct trucking company drivers association (dtcda) suka fitar, wadda ta nemi a yi watsi da yajin aikin.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin tarayya ta gayyaci Ɗangote da shugabannin NUPENG kan batun yajin aiki

Ta ce wannan ƙungiyar wata ƙirƙira ce da kamfanin dangote da abokan huldarsa suka samar domin hana direbobi kusan dubu goma shiga NUPENG.

kungiyar ta bayyana cewa shugabanta, enoch Kanawa, lauya ne ba direba ba, kuma asalinsa tsohon jami’in ƙungiyar masu motocin haya ta ƙasa (NARTO) ne, wanda daga baya ya yi aiki da kamfanin Mrs Energy na sSayyu Dantata.

NUPENG ta zargi shi da amfani da wannan ƙungiya da aka kafa domin rikita al’umma da yada ƙarya.

NUPENG ta yi gargadin cewa ko da bautar bayi ta gushe ƙarni da suka wuce, wasu masu neman riba suna ƙoƙarin dawo da ita ta hanyar tauye haƙƙin ma’aikata.

Ta ce kowane ɗan ƙasa ya guji goyon bayan irin wannan tsarin bautar kai tsaye.

A ranar 5 ga watan satumba, NUPENG ta sanar da cewa za ta fara yajin aiki daga ranar 8 ga watan, kuma ma’aikatanta za su fara neman wasu ayyuka daban.

Sai dai rassa na PTD da kuma DTCDA sun bayyana cewa ba za su shiga yajin aikin ba, suna masu cewa hakan ba zai amfani ‘yan ƙasa ba.

kungiyar NUPENG ta jaddada cewa babu rarrabuwar kai a cikinta, kuma haɗin kan ta yana nan daram duk da ƙoƙarin da ake yi na rura rikici daga masu son zuciya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here