Gwamna Uba Sani ya ce El-Rufai ba shi ne jagoransa a siyasa ba

Sani El rufai 1 750x430

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa ba a karkashin koyarwar tsohon gwamna Nasir El-Rufai yake siyasa ba, inda ya ce shugabanninsa a siyasa tun farko sune shugaban ƙasa Bola Tinubu da marigayi lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Gani Fawehinmi.

Uba Sani ya bayyana haka a shirin siyasa na TVC, inda ya ce abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne samar da kyakkyawan mulki a Kaduna ba maganar mutane ba.

Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 1994 ya haɗu da Tinubu a gidan Beko Ransome-Kuti, sannan kuma ya rayu tare da Gani Fawehinmi a lokacin gwagwarmayar kare dimokuraɗiyya.

Gwamnan ya ce ba ya son tattauna batun mutane, domin burinsa shi ne ci gaban jihar Kaduna.

Dangane da zargin cewa gwamnatinsa tana biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga, Sani ya musanta hakan, inda ya bayyana shi a matsayin ƙarya da wasu ‘yan siyasa ke yaɗawa domin neman amfaninsu.

Labari mai alaƙa: Rashin Tsaro: El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da ƙarfafa ayyukan ƴan bindiga

Ya ce ba a biyan kobo ba, sai dai gwamnati ta haɗa dabarun soji da na zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da shugabannin al’umma da hukumomin tsaro, musamman a Birnin Gwari inda ake samun sauƙi.

Game da rikicin da ya barke a wani taron jam’iyyar adawa kwanan nan, gwamnan ya nesanta kansa daga lamarin, yana mai cewa a matsayinsa na wanda ya sha tsarewa saboda gwagwarmayar kare doka, ba zai taɓa shiga wani abu da zai hana wasu yin harkar siyasa ba.

Haka kuma ya tunatar da maganar marigayi Gani Fawehinmi cewa dole ne a girmama ‘yan sanda domin kauce wa rikici. Don haka ya roƙi a bar su su gudanar da bincikensu kan abin da ya faru.

Gwamna Uba Sani ya kuma nuna nasarorin da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen da ya gabata a matsayin hujjar cewa gwamnati tana tafiya bisa haɗin kai.

Ya ce jam’iyyar ta lashe kashi 70% na kujeru a Kaduna, ciki har da Chikun da Kajuru, inda a baya ba ta taɓa cin zaɓe ba, alamar cewa gwamnati ba ta tafiya bisa addini ko ƙabila ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here