
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce zai zama shugaban kasa abin kwatance ga al’ummar Igbo matukar aka zabe shi a 2023.
Abubakar ya yi wannan alkawarin ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na shiyyar Kudu maso Gabas ranar Talata a Enugu.
Ya ce soyayyarsa ga Ndigbo tana da matukar tasiri, a zaben 2011 da 2019 kuma ya zabi mazan Igbo a matsayin abokan takara.
Abubakar ya kara da cewa ya zabi dan kabilar Ibo, gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 .
“Don haka me ya sa ake cewa ba zan baiwa Igbo dama su jagoranci kasar nan ba bayan na zama shugaban kasa.
“Na yi haka a shekarar 2019 lokacin da na dauko Obi a 2011 da kuma 2023 na zabi Ifeanyi Okowa, wani dan kabilar Igbo a matsayin abokina, ko da Ohaneze ya ce babu wani Igbo da ya isa ya tsaya takarar Shugaban kasa a karkashin PDP.
Ya ce akwai bukatar a mayar da kasar nan abin sha’awa don sanya ‘yan kasa su zauna tare da kuma ba da gudummawar kason su don ci gabanta.
Atiku Abubakar ya ce, idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta samar da ingantaccen ilimi wanda zai bawa matasa damar zama kwararrun da ake bukata abangaren tattalin arzikin zamani.
Dan takarar shugaban kasar na PDP ya kuma yi alkawarin cewa zai samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya idan aka zabe shi .












































