Yakin neman ZABE a Fadoji da Masallatai da Majami’ai ya sabawa dokar zaben 2022-Lauya

Political Parties
Political Parties

Wani Lauyan masanin doka da tsarin mulkin kasa, Mista Kayode Ajulo, ya gargadi ‘yan siyasar Najeriya da jam’iyyun siyasa kan kada su bijirewa tanade-tanaden dokar zabe ta 2022, musamman dangane da gudanar da yakin neman zaben.

Ajulo ya tunatar da ‘yan takarar da ke neman mukamai daban-daban a zabukan da ke tafe da cewa bisa ga tanadin dokar zabe, an sanya takunkumi da yawa da nufin magance magudin zabe da aka saba farawa a lokacin yakin neman zabe.

Lauyan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ranar Laraba a Abuja, ya bukaci ’yan siyasa da jam’iyyu da sauran kungiyoyin yakin neman zabe da su kaucewa yakin neman zabe a fadar sarakunan gargajiya dake fadin kasar.

Ya ce fadojin wuri ne da jama’a ke ba da kudade, kuma bai kamata a yi amfani da su a matsayin filin yakin neman zabe ba, ya kara da cewa irin wannan rashin biyayya ga dokar zabe zai haifar da mummunan sakamako.

Lauyan, yayin da yake karanto Wani sashe ya ce: “Sashe na 92 ​​na dokar zabe ta 2022, ya tanadi haramta wasu halaye a yakin neman zabe.

Ya ce ya wajaba cewa yakin neman zabe ko taken siyasa ba za a gurbata shi da kalaman batanci kai tsaye ko a fakaice ba, wadda yin hakan zai iya cutar da addini ko kabila ko kuma bangare.

Haka Kuma ba a yadda ayi amfani da kalaman batanci ko son zuciya ko zage-zage ba, su zasu iya haifar da tashin hankali a yakin neman ZABE.

Ya ce ba za a yi amfani da wuraren da aka kebe domin ibada ko ofisoshin ‘yan sanda da ofisoshin gwamnati ba wajen yakin neman zabe.

Sauran sun hada da: gangami da jerin gwano; ko Kuma haddasa kai hari ga takwarori sauran jam’iyyun siyasa ko ‘yan takara ko kuma shirye-shiryensu.

Ya ce zabe mai inganci shi ke kasancewa ginshikin adalci ga kowace gwamnati a tsarin dimokuradiyya.

Ajulo ya ce Najeriya na da tarihin zabuka masu cike da shubuha tun bayan zaben farko da aka yi bayan samun ‘yancin kai a Shekarar 1965.

Ya ce tun a wancan lokacin, duk zabukan kasar nan sun kasance da wani nau’i na rashin gaskiya, yayin da ya bukaci jam’iyyun siyasa da su yi taka-tsantsan da kuma bin doka da Oda.

Kamfanin dillancin Labaran ya rawaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe ta 2022, a ranar 25 ga watan Faburairu inda ta soke dokar zabe ta 2010.

Sassa na 92 da 93 da 94 da 95 da Kuma 96 na sabuwar dokar zabe sun yi hani tare da samar da hukunci Mai tsanani ga wanda aka samu yana gudanar da yakin neman zabe a wuraren ibada ko fadoji da da wuraren da ke da ofisoshin gwamnati.

Haka Kuma tsoratarwa da sayan kuri’u da magudi ko yin amfani da jabun katin zabe ko kwace akwatin zabe da sauran laifukan zabe Duk wanda aka samu zai fuskanci hukunci.

Sashi na 92(3) ya ce, “Ba za a yi amfani da wuraren da aka kebe domin ibadar ko ofisoshin ‘yan sanda da ofisoshin gwamnati ba wajen yakin neman zabe, da gangamin siyasa ba.”

NAN ya kuma rawaito cewa, Mista Festus Okoye, kwamishinan hukumar zaben Kuma Shugaban sashen yada labarai da wayar da kan jama’a, ya gargadi ‘yan siyasa kan su guji yakin neman zabe a Majami’ai da Masallatai da sauran wuraren taruwar jama’a.

Tawagar yakin neman zaben jam’iyyar PDP ya kunshi mambobi 325 tare da Gwamna Udom Emmanuel a matsayin babban darakta, yayin da kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar APC ta kunshi mutane 442 tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, su ne mataimakan shugabanni.

A yayin da ake gudanar da yakin neman zabe, Jam’iyyu da ‘Yan takararsu sun shirya tsaf domin shiga yankunan abokan hamayyar su tare da kokarin tabbatar da yada manufofin su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here