Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da dakatar da Kwamishinan Lafiya na jihar, Alhaji Yunusa Musa-Ismail, daga mukaminsa nan take.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Malam Yahaya Sarki, ya fitar a Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Sarki ya bayyana cewa dakatarwar ta biyo bayan umarnin da gwamnan ya bayar, inda ya bukaci Musa-Ismail ya bayar da hujjoji masu ƙarfi kan dalilin da zai sa kada a ɗauki matakan ladabtarwa a kansa saboda zargin sakaci da rashin bin umarnin da ke kan nauyin sa a matsayin kwamishina.
“Da wannan umarni, an dakatar da kwamishinan daga mukaminsa har sai baba-ta-gani,” in ji sanarwar.
Karanta: Sanatoci daga jihar Kebbi sun koma APC bayan sun gana da shugaba Tinubu
Gwamnan ya sake jaddada cewa gwamnatin sa ta kuduri aniyar tabbatar da gaskiya, ladabtarwa, da ingantaccen gudanar da ayyuka a dukkan bangarori.
A cewar Sarki, Idris ya nuna cewa dole ne jami’an gwamnati su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar nuna nagarta da rikon amana.
NAN









































