Gwamna Siminalayi Fubara, a ranar Juma’a, ya roki kotun daukaka kara da ta yi watsi da hukuncin da ya hana Babban Bankin Najeriya (CBN) fitar da kason kudi na wata-wata ga Rivers.
Gwamnan, ta bakin lauyansa Yusuf Ali, SAN, ya roki kwamitin mutum uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin Mai shari’a Hamma Barka, da ya janye hukuncin babban kotun da ya ce an bayar da shi cikin rashin imani.
Ya bukaci kotun daukaka kara da ta ba da damar daukaka kara mai lamba CA/ABJ/CV/1303/2024 tare da soke umarnin da mai shari’a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya ta yi wa jihar a hukuncin da ta yanke a ranar 30 ga watan Oktoba.
Bukatun Fubara ya zo ne a ranar da kwamitin da Mai Shari’a Barka ya jagoranta ya hada wasu kararraki biyar da suka taso daga hukuncin da babbar kotun ta yanke.













































