Kotun Koli Ta Soke Dokar Da Ta Halarta Yin Caca A Najeriya

Supreme Court of Nigeria 1

Kotun Koli ta soke dokar data Halarta yin caca a Najeriya wadda Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta kafa a shekarar 2005.

A hukunci na bai daya da wasu alkalai bakwai na kotun kolin, mai shari’a Mohammed Idris ya karanta, ya ce majalisar dokokin kasar ba ta da hurumin yin doka a kan batutuwan da suka shafi caca da wasannin kwata-kwata.

Kotun ta ce irin wannan ikon yana hannun Majalisar Dokokin Jihohi ne kawai, wadanda ke da hurumin kebantaccen iko kan caca da wasannin kwatsam.

Mai shari’a Idris ya ba da umarnin a daina aiwatar da dokar caca ta 2005 a duk jihohi, sai dai babban birnin tarayya Abuja, wanda majalisar ta ba da ikon yin doka.

A shekarar 2008 ne babban mai shari’a na jihar Legas ya shigar da karar a kan gwamnatin tarayya game da wanda ke kula da harkokin wasanni da caca.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here