Malamai 4,169 sun fadi a jarrabawar hukumar TRCN

IMG 20250529 WA0013

Kimanin malamai 4,169 a fadin kasar nan suka fadi a jarrabawar da hukumar yi wa malamai rijista ta kasa TRCN ta rukunin ‘A’ ta bana da aka rubuta a tsakanin ranakun 15 zuwa 17 ga watannan da muke ciki na Mayu.

Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a birnin tarayya Abuja mai dauke da sa hannun Daraktar tabbatar da kwarewa da bayar da Lasisi Dakta Jacinta Ezeahurukwe.

Ta ce, kimanin malamai 13,782 ne suka yi rijistar rubuta jarrabawar, amma mutum 12,874, kimanin kaso 93.4 ne suka rubuta, yayin da mutane 908 watau kaso 6.6 ba su zauna rubuta jarrabawar ba.

Haka kuma ta kara da cewa, kimanin mutane 8,705 cikin wadanda suka rubuta jarrabawar ne suka samu nasara watau kimanin kaso 67.62 tyayin da kaso 32.38 watau mutum 4,169 suka fadi jarrabawar.

Ezeahurukwe ta kara da cewa, jihar Lagos ce kan gaba wajen wadanda suka samu nasarar har kashi 80 inda Edo ke rufa mata baya da kaso 73.3 sai Niger mai kaso 69.2 sai kuma birnin tarayya Abuja mai kaso 68.3

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here