Wata maniyyaciya yar Najeriya Hajiya Zainab, yar asalin jihar Plateau ta mayar da kudi kimanin Dalar Amurka dubu biyar ga mai su dan a kasar Rasha bayan da ta tsince su a kasar saudiyya.
A daren ranar Talatar da ta gabata ne maniyyaciyar ta tsinci kudin a masallacin Harami na birninn Makkah, wadanda suka kai adadin kimanin Naira Miliyan 8 da dubu dari biyu da arba’in a kan canjin kudin Najeriya idan aka canjar da duk Dala 1 a kan naira dubu daya da dari shida da arba’in da takwas.
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Plateau karkashin jagorancin Alhaji Daiyabu Dauda, da kuma hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON, ne suka tabbatar da faruwar lamarin.
Alhaji Daiyabu Dauda, ya ce, wannan hali da matar ta nuna abun a yaba ne da kuma jinjinawa.












































