Sanata Shekarau ya duba ayyuka, tare da kaddamar da wasu guda 11 a Kano 

Sh aa senator
Sh aa senator

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau a ranar Litinin ya duba tare da kaddamar da ayyuka 11 a kananan hukumomi 7 na cikin birnin Kano.

Solacebase ta ruwaito cewa kananan hukumomin sun hada da Gwale, Minjibir, Nassarawa, Dala, Kumbotso, Municipal da Tarauni inda ayyukan suka ta’allaka ne kan fannin ilimi da lafiya.

Da yake jawabi ga manema labarai a yayin rangadin ayyukan, Malam Ibrahim Shekarau, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne a karo na biyu, ya ce gaba daya ayyukansa na 2020 da 2021 sun ta’allaka ne kan ilimi da lafiya, domin shi ne babban kalubalen al’ummar mazabar sa, don haka ya mayar da hankali wajen inganta bangarorin biyu.

“Kamar yadda kuke gani, kashi 90 cikin 100 na ayyukan gina ajujuwa ne kuma mai yiwuwa kashi 10 cikin 100 na da alaƙa da lamuran kiwon lafiya.

Dalilina na mayar da hankali kan harkokin ilimi tun lokacin da na je majalisar dattawa shi ne, ilimi shi ne mafi girman abu da za ka iya ba wa kowane dan kasa. Idan ka samar da isassun makarantu, za a samu isassun damammaki da yaranmu za su yi karatu. Kuma idan dalibai suna da ilimi, to al’umma za su inganta.

“Muna da kwamitoci da ke zuwa kananan hukumomi su kawo mana rahoton bukatun al’umma.”

‘’Wannan wata hanya ce da muka samar don fahimtar abin da mutanenmu ke bukata ba abin da muke tunanin suna bukata ba; Ayyukan da aka duba tare da kaddamar da su sun hada da: Gina tare da sama da katangar ajujuwa 2 masu dauke da ofisoshi da shaguna a makarantar firamare ta Kawon Alhaji Sani; Duban aikin tsawaita aikin kantin magani na Accident and Emergency (A & E) a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH); gina tare da samar da katangar ajujuwa 2 masu dauke da ofisoshi da kantin sayar da kayayyaki a makarantar firamare ta makiyaya, Sheka; da kuma gyara makarantar ’yan mata ta Maryam Shekarau, Kwalli, Sabuwar Kofa.

Gina ajujuwa guda 2 tare da ofishi da kantin sayar da kayayyaki a makarantar firamare ta A.A Sule lokon makera; aza harsashin ginin katangar ajujuwa guda 2 mai ofishi da shago a Diso da kuma duba wani katanga na ajujuwa 3 masu dauke da ofisoshi da kantin sayar da kayayyaki a makarantar Ta’adibul Aulad Girls Islamic secondary school, Adakawa.

Sauran sun hada da gina katanga na ajujuwa 3, ofis da shaguna a makarantar sakandiren mata ta gwamnati, Kunya a Minjibir; Duban aikin gina kwalejin kur’ani a Gunduwawa; Gina ajujuwa guda 3 wanda aka tanada da ofis a makarantar firamare ta musamman ta Gunduwawa da Gina cibiyar kula da lafiya matakin farko mai gadaje 20 a unguwar Babawa unguwar Gunduwawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here